Mutane 14 sun kwashe kusan kwanaki 40 a gidan yari kan zargin yi wa wani jami’in gwamnati ihu a Borno
Daga Wakiliya
Wani lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Hamza Nuhu Dantani, ya nuna damuwa kan tsare wasu mutane kusan 14 da ake zargin an kama su bayan sun yi ihu da katse jawabin wani jami’in gwamnati a Jihar Borno.
Dantani ya ce mutanen sun shafe kusan kwanaki 40 a gidan yari a Maiduguri, yayin da ake tuhumarsu da laifukan da suka haɗa da yin ihu, katsewa da kuma kunyata jami’an gwamnati yayin wani taro,
Lauyan ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Borno ta umurci wata kotu da kada ta bayar da belin waɗanda ake tuhuma
Ya ce idan zargin gaskiya ne, hakan na iya zama katsalandan ga aikin shari’a tare da tauye haƙƙin waɗanda ake tsare da su.
Dantani ya tambayi yadda yin ihu ko nuna rashin amincewa da jawabin jami’in gwamnati zai zama laifi, yana mai cewa waɗanda ake tuhuma na da haƙƙin samun adalci da kuma a ɗauke su a matsayin marasa laifi har sai an tabbatar da laifinsu.




