Wannan Ya Wuce Kuskuren Furuci” -Barau Ya Ki Karɓar Afuwar Aisha Humaira Kan Bidiyon Yaran Rarara, Ya Ce: “Su Haɗu a Kotu”

DA DUMI-DUMI

Wannan Ya Wuce Kuskuren Furuci – Mu Hadu a Kotu Kawai – Barau Ya Ki Karɓar Afuwar Aisha Humaira Kan Yaran Rarara

Bangaren Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi watsi da neman afuwar da jarumar Kannywood Aisha Humaira ta yi a madadin matan mawaki Dauda Kahutu Rarara da suka yi kalaman da suka jawo ce-ce-ku-ce.

Da yake magana a Freedom Radio Kano, babban hadimin Sanata Barau, Salisu Officer, ya ce zargin da aka yi wa Sanata Barau na hannu a ta’addanci ba abu ne da za a ce kuskuren furuci ne kawai ba.

A cewarsa, zargin ta’addanci laifi ne mai girma, don haka ba za su amince da neman afuwa kawai ba.

Ya ce sun kuduri aniyar ci gaba da bin lamarin ta hanyar doka.Salisu Officer ya bayyana cewa za su bukaci ‘yan sanda su gudanar da cikakken bincike domin gano mutanen da suka shirya tare da daukar nauyin yada irin wadannan zarge-zarge.

Ya kuma ce matan da suka yi kalaman dole ne su bayyana wanda ya rubuta musu abin da suka fada. Idan kuma sun yi hakan da kansu, za su fuskanci hukuncin doka.

A cewarsa, zargin da aka yi wa Sanata Barau ya shafi bata suna da kuma wani babban laifi da dokokin Najeriya ba sa dauka da wasa.Sai dai ya jaddada cewa wannan batu ba zai rage wa Sanata Barau farin jini ko tasirinsa a siyasa ba.

Haka kuma ya gargadi matasan Arewa da kada su karbi kudi domin yada karya ko shiga ayyukan da za su iya jefa su cikin matsala da doka.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img