Sabon Rikici Ya Kunno Kai Tsakanin Tinubu da Trump: Amurka Ta Kakaba Harajin Kashi 12.5% Kan Kayayyakin Najeriya

DA DUMI-DUMI

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Tsakanin Tinubu da Trump: Amurka Ta Kakaba Harajin Kashi 12.5% Kan Kayayyakin Najeriya Saboda Zargin Ana Bautar Da Jama’a

Gwamnatin Amurka ta sanya sabon harajin shigo da kaya na kashi 12.5% kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Najeriya zuwa Amurka, tana mai cewa ƙasar ba ta da dokoki ko kuma ba ta aiwatar da isassun matakan hana shigar da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas ko bautarwa ba (forced labour).

Hukumar Kasuwancin Amurka (USTR) ce ta sanar da matakin, bayan binciken da ta ce ta gudanar kan manyan abokan hulɗar kasuwancin Amurka 60 ƙarƙashin Sashe na 301 na Dokar Kasuwanci.

A cewar USTR, ƙasashen da suka riga suka haramta ko suka yi alƙawarin hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar bautarwa ko aikin tilas za su fuskanci harajin 10% kacal.

Waɗannan sun haɗa da Indiya, Indonesiya, Malaysia, Mexico da Birtaniya.

Sai dai Najeriya na cikin ƙasashen da za a kakaba musu harajin 12.5%, ban da wasu kayayyakin da aka ware daga wannan mataki.

Shugaban Hukumar Kasuwancin Amurka, Jamieson Greer, ya ce matakin na da nufin tilasta wa ƙasashen duniya su ƙarfafa dokokin da ke yaƙi da amfani da aikin tilas (bautar da jama’a) wajen samar da kayayyaki.

Sai dai USTR ta bayyana cewa ba za a sanya harajin kan wasu kayayyaki ba, musamman waɗanda za su iya haddasa ƙarancin albarkatun ƙasa, tangarɗa ga tattalin arzikin Amurka, ko kuma waɗanda ba a iya samar da su cikin isasshen adadi a cikin ƙasar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img