“Ta baya yake saduwa da ni, har lokacin al’ada sai ya neme ni; ya shafa mini cututtuka, ya kwace mini fasfo, shi ya sa na gudu gidan Gumi ceton rayuwa ta” – Matar Nasiru Idris yar Morocco ta bayyana wa kotu
Daga Wakiliya
Wata ’yar ƙasar Morocco, Khadija Diab, wadda ke neman a raba aurenta da ɗan Kaduna, Nasiru Idris, ta bayyana cewa ta gudu daga gidan mijinta ne saboda tsoron lafiyarta da rayuwarta.
A cikin bayanan da ta gabatar wa Kotun Shari’a da ke Kaduna kamar yadda Wakiliya ta ruwaito daga Jaridar Premium Times, matar ta zargi mijinta da tilasta mata yin jima’i ta dubura, da kuma neman yin jima’i da ita a lokacin da take cikin al’ada.
Ta ce abin ya jawo mata ciwo da matsananciyar damuwa, sannan ta zargi mijin da yawan shafa mata cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i (STDs).
Matar ta kuma zargi mijin da ƙin kai ta asibiti domin neman magani, inda ta ce a maimakon haka yana tilasta mata yin amfani da magungunan gargajiya ko wanda ba a rubuta mata ba.
A cewar takardun kotun, ta kuma yi zargin cewa mijin ya kwace mata fasfo ɗinta, lamarin da ta ce ya hana ta samun ’yancin komawa ƙasarta ta Morocco ko ziyartar iyalanta.
Ta ce saboda waɗannan matsaloli ne ta bar gidan mijinta ta nemi mafaka a gidan Sheikh Ahmad Gumi da matarsa, wadda ita ma ’yar ƙasar Morocco ce.
Ta bayyana cewa Gumi da matarsa ne kawai mutanen da ta sani a Najeriya ban da mijinta, don haka ta ga gidan nasu a matsayin wurin da za ta samu mafaka.
Zargin “kwace mata”
Nasiru Idris ya zargi Sheikh Gumi da ƙwace masa matarsa, yana cewa bayan ya kai matar wurin Gumi domin neman shawara da sulhu, ta daina amsa kiransa.
Ya ce matarsa ta kwashe kusan watanni 11 a wajen Gumi, yana zargin malamin da riƙe ta ba bisa ƙa’ida ba.
Sai dai Sheikh Gumi ya musanta zargin, yana cewa matar ta je gidansa ne da kanta domin neman mafaka daga cin zarafin da ta ce tana fuskanta a gidan aure.
Abin da matar ke nema a kotu
Matar ta shigar da ƙarar neman a raba aurensu, bisa zargin hana ta haƙƙin aure, rashin ciyarwa da kula da ita, cin zarafi da kuma tilasta mata ayyukan da ta bayyana a matsayin haram.
Ta kuma roƙi kotu ta umarci mijin ya mayar mata da fasfo ɗinta da kayanta, tare da ba ta damar komawa Morocco.
A gefe guda, Sheikh Gumi ya ce shi ma ya shigar da ƙara kan Nasiru Idris bisa zargin ɓata masa suna.
Dukkan zarge-zargen da ke cikin wannan rahoto dai bayanai ne daga ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar wa kotu




