Daga 1 ga Octoba WhatsApp zai fara cazar kuɗi kan saƙonnin da ake tura wa na kasuwanci
Daga Wakiliya
Kamfanin Meta, mai WhatsApp, ya sanar da cewa daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, zai fara karɓar kuɗi kan wasu saƙonnin da ‘yan kasuwa ke aikawa wa kwastomominsu ta manhajar WhatsApp.
Sabon tsarin zai shafi kamfanoni da ke amfani da WhatsApp Business Platform, wadda aka fi sani da WhatsApp Business API, wajen tura saƙonni ga dimbin kwastomomi.
Ba zai shafi masu amfani da WhatsApp na yau da kullum ba, kuma ba zai sanya masu amfani da manhajar WhatsApp Business ta yau da kullum su fara biyan kuɗi ba.
A Najeriya, rahoton ya ce saƙon da ke ƙarƙashin nau’in service/utility zai kai kusan dala $0.0101, wato kimanin Naira 14, yayin da saƙonnin talla za su fi tsada, inda za su kai kusan dala $0.062, kwatankwacin Naira 84 ga kowane saƙo.
Misali, idan wata kamfanin fasahar kuɗi a Najeriya ya aika saƙonni 500,000 da ake caji, zai iya kashe kusan dala $5,050 a matsayin kuɗin saƙonnin Meta kaɗai.
Wannan sabon tsarin na iya shafar bankuna, kamfanonin fintech, kamfanonin jiragen sama, ‘yan kasuwa, kamfanonin sadarwa da sauran ƙananan da manyan ‘yan kasuwa da ke amfani da WhatsApp wajen hulɗa da kwastomomi.
A halin yanzu, WhatsApp na ba wa wasu kamfanoni damar aika saƙonnin sabis kyauta cikin wa’adin sa’o’i 24 bayan kwastoma ya fara hulɗa da su.
Sai dai daga Oktobar 2026, za a cire wasu daga cikin wannan damar ta kyauta, lamarin da zai sa kamfanoni su riƙa biyan kuɗi gwargwadon adadin saƙonnin da suka aika.
Meta ta fara sauya tsarin farashin WhatsApp Business tun watan Yulin 2025, lokacin da ta sauya daga tsarin cajin kowace tattaunawa zuwa tsarin cajin kowane saƙo ga wasu saƙonnin da kamfanoni ke farawa.
Masana harkokin kasuwanci na ganin sabon tsarin zai iya sa ƙananan kamfanoni da sabbin ‘yan kasuwa su ƙara taka-tsantsan wajen amfani da WhatsApp wajen tallace-tallace da hulɗa da kwastomomi.
Farashin saƙonnin zai kuma bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, gwargwadon inda wanda ake aikawa wa saƙon yake da kuma nau’in saƙon.
Sai dai sabon tsarin ba yana nufin WhatsApp za ta fara cajin kuɗi ga talakawan da ke amfani da manhajar ba.
Mutanen da ke amfani da WhatsApp na yau da kullum za su ci gaba da aikawa da karɓar saƙonni ba tare da wannan sabon cajin ba.
Canjin ya fi shafar kasuwancin da ke amfani da WhatsApp Business Platform wajen gudanar da hulɗa da kwastomomi a babban sikeli.





