Aisha Humaira Ta Ba Sanata Barau Jibrin Haƙuri Kan Bidiyon Cin Mutunci da Yaran Rarara Suka Yi Akansa

DA DUMI-DUMI

Aisha Humaira Ta Ba Sanata Barau Jibrin Haƙuri Kan Bidiyon Da Yaran Rarara Suka Yi Akansa Na Cin Mutunci Da Danganta Shi Da Ta’addanci

Jarumar Kannywood Aisha Humaira, matar fitaccen mawakin siyasar APC Dauda Kahutu Rarara, ta nemi afuwar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, kan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta inda wasu mata masu yi wa Rarara rakiya suka yi kalaman da suka haɗa sunan Barau da ta’addanci.

A cikin bidiyon da ya jawo ce-ce-ku-ce, wata mata mai suna Zara tare da wasu abokan rakiyarta sun rika yi wa Sanata Barau Jibrin kirari da zarge-zarge, suna kiran sa “matsalar Arewa, matsalar APC” tare da zargin cewa yana goyon bayan ‘yan ta’adda, lamarin da ya fusata magoya bayansa.

Sai dai a wani sabon bidiyon neman afuwa da ta fitar cikin harshen Hausa, Aisha Humaira ta ce abin da aka yi bai dace ba, tana mai bayyana cewa kalmar “ta’addanci” da aka ambata kuskure ne da bai kamata a furta ba.

Ta bayyana Sanata Barau Jibrin a matsayin uba a gare su, tana mai tunatar da irin alherin da ya yi wa iyalinsu, inda ta ce ya yi tafiya daga Abuja zuwa Maiduguri domin zama Wakili a wajen aurenta da Rarara.

Aisha Humaira ta kuma nemi afuwar Sanata Barau Jibrin, iyalansa, magoya bayansa da daukacin ‘yan APC, tana roƙonsu da su yi haƙuri tare da amincewa cewa an yi masa ba daidai ba.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Sanata Barau Jibrin da Dauda Kahutu Rarara ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan neman afuwa ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img