🤔 Ko Kun San…?
A shekarar 2016, ‘yan sandan birnin Lima da ke jihar Ohio a Amurka sun wallafa hoton wani mutum da ake nema ruwa a jallo mai suna Donald “Chip” Pugh, bayan ya gaza halartar zaman kotu.
Sai dai maimakon ya É“uya, Donald ya yi abin da ba a saba gani ba. Inda ya aike wa ‘yan sanda da wani sabon selfie nasa, yana cewa:
“Ga hoto na mai kyau ku canza. Wanda kuka saka ba ya min kyau kwata-kwata.” 😂
Abin mamaki kuwa, ‘yan sandan ba su goge saÆ™on ba. Maimakon haka, suka sake wallafa sabon hoton tare da yi masa godiya cikin barkwanci, suna cewa sun gode da “haÉ—in kansa”, amma har yanzu suna son ya miÆ™a kansa ga hukuma.
Lamarin ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, inda dubban mutane suka yi ta rabawa da yin dariya kan abin.
Sai dai duk da sabon hoton da ya tura, bai tsira daga kamu ba. Inda bayan ‘yan kwanaki, jami’an tsaro suka kama Donald Pugh a jihar Florida.





