Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Najeriya Ba Ta da Tattalin Kula da Abubuwan Da Aka Gina, Shi Yasa Kasar Ta Kasa Ci Gaba – Okonjo-Iweala

Daga Wakiliya

Daraktar Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce Najeriya na fama da rashin kyakkyawar al’adar kula da ababen more rayuwa da aka gina, lamarin da ke hana ƙasar samun cikakkiyar ci gaba.

Okonjo-Iweala ta bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da take jawabi a Taron Tattalin Arziki da Zuba Jari na Jihar Delta na 2026 da aka gudanar a Asaba.

Ta ce arzikin ƙasa ko ware kuɗaɗe a kasafin kuɗi kaɗai ba sa tabbatar da samun ingantattun tituna ko kula da su yadda ya kamata.

“Mu a Najeriya ba mu da kyakkyawar al’adar kula da abubuwan da muka gina. Ni ma ‘yar Najeriya ce, amma dole ne mu faɗi gaskiya,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa Najeriya na buƙatar inganta tashoshin jiragen ruwa, samar da ingantattun hanyoyin sadarwar zamani, da rage tsadar kasuwanci domin bunƙasa tattalin arziƙi.

A cewarta, abin da ya fi muhimmanci ba wai tsara manufofi kawai ba ne, illa aiwatar da su yadda ya kamata tare da ba wa abubuwan da suka fi muhimmanci fifiko.

DA DUMI-DUMI

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Gaggawar Yaɗa Labaran da Ba a Tantance Ba Ka Iya Shafar Kasuwar Makamashi da Zuba Jari, Ya Jawo Tashin Farashi – NUPRC Ta Gargadi...

A ƙarshe, ta buƙaci 'yan jaridar da ke ba da rahotannin makamashi su mayar da hankali kan tantance bayanai, fahimtar alkaluma da kuma bayar da cikakken mahallin labari domin tabbatar da sahihanci da ƙarfafa amincewar jama'a.

Wani Mutum da ‘Yan Sanda Suka Baza Hotonsa Suna Nemansa Ruwa a Jallo Ya Sake Aika Musu Sabon Hoto, Ya Ce Wanda Suka Saka...

"Ga hoto na mai kyau ku canza. Wanda kuka saka ba ya min kyau kwata-kwata."

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa ‘yan siyasa...

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa 'yan siyasa addu'a -Dr. Ahmed Gumi

An Kashe Biliyoyin Naira Amma Duk da Haka Cibiyoyin Lafiya 6,516 Sun Gagara Aiki a Najeriya; Arewa Ce Kan Gaba

Jihar Katsina ce ke da mafi yawan cibiyoyin da ba sa aiki da guda 442, sai Osun da 406, yayin da Benue ke da 343, Enugu 335, Adamawa 286, sannan Borno na cikin jerin jihohin da ke fuskantar matsala.

Kanun Labarai

Kasar Guinea Ta Fice Daga Shirin Samar da Kuɗin Bai Ɗaya na ECOWAS -Ta Zabi Riƙe Kuɗinta

Ana sa ran shugabannin ECOWAS za su sake ganawa a watan Disamba domin tattauna sauran batutuwan da suka rage kafin fara amfani da kuɗin Eco.

Gaggawar Yaɗa Labaran da Ba a Tantance Ba Ka Iya Shafar Kasuwar Makamashi da Zuba Jari, Ya Jawo Tashin Farashi – NUPRC Ta Gargadi...

A ƙarshe, ta buƙaci 'yan jaridar da ke ba da rahotannin makamashi su mayar da hankali kan tantance bayanai, fahimtar alkaluma da kuma bayar da cikakken mahallin labari domin tabbatar da sahihanci da ƙarfafa amincewar jama'a.

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa ‘yan siyasa...

Malamin da ya shiga siyasa, aka yi ƙwaramniyar siyasa da shi, ya fi malamin da ya zauna kan buzun yana yi wa 'yan siyasa addu'a -Dr. Ahmed Gumi

An Kashe Biliyoyin Naira Amma Duk da Haka Cibiyoyin Lafiya 6,516 Sun Gagara Aiki a Najeriya; Arewa Ce Kan Gaba

Jihar Katsina ce ke da mafi yawan cibiyoyin da ba sa aiki da guda 442, sai Osun da 406, yayin da Benue ke da 343, Enugu 335, Adamawa 286, sannan Borno na cikin jerin jihohin da ke fuskantar matsala.

Tsadar Sadaki Na Sa Matasa Da Dama Gujewa Yin Aure – Shugaban Uganda Ya Gargadi Iyaye Su Rage Sadakin ‘Ya’yansu

Ku mutanen Banyankole kuna lalata ci gaban yawan jama'a. Iyaye, me ya sa kuke sayar da 'ya'yanku? Shanu 16, ban ma san adadin sauran ba. Me ya sa dole ne ku tara dukiya ta hanyar 'ya'yanku? Me ya sa ba za ku yi aiki ku sami abin ku da kanku ba?" in ji Museveni.

Kada A Rika Ba Jarirai Yan Ƙasa da Wata Shida Abinci Mai Tauri Kamar Tuwo, Koko, Kunu ko Fura – Likitocin Yara Sun Gargadi...

hakan na iya jefa su cikin haɗarin ƙarancin jini (anaemia), kamuwa da cututtuka da kuma shaƙewa.

NACCIMA Ta Buɗe Shirin Bayar da Rancen Dala Miliyan 150 Ga Kamfanonin Najeriya

NACCIMA ta ce shirin na da nufin sauƙaƙa wa kamfanonin Najeriya samun jari na dogon lokaci daga ƙasashen waje domin bunƙasa masana'antu da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img