Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo Ya Kammala Karatun Sunan Abu Dawud Bayan Shekaru 10

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Farfesa Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, ya kammala koyar da littafin Sunan Abu Dawud bayan shafe kusan shekaru 10 yana gabatar da darussansa.

An gudanar da taron kammala karatun ne a gaban manyan malamai, malaman jami’o’i, ɗalibai da baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya.

Sunan Abu Dawud na daga cikin manyan littattafan Hadisi guda shida da ake kira Kutub al-Sittah, wanda ya ƙunshi hadisai kan ibada, fikihu, kyawawan ɗabi’u da sauran fannoni na rayuwar Musulmi.

Maharta sun bayyana cewa manyan malamai, furofesoshi, likitoci da masu bincike kan harkokin Musulunci kan riƙa zuwa Kano domin halartar darussan, inda wasu ma suke sauka a otal domin kada su rasa karatun.

Bayan kammala darasin, Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya ƙaddamar da sabon littafinsa mai suna “Naylul Maqsud bi Khatmi Sunani al-Imam Abi Dawud.”

Masu halarta sun yabawa gudunmawar Sheikh Rijiyar Lemo wajen bunƙasa ilimin Hadisi, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, tsawon rai da albarka a iliminsa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img