Yar fim Halima Abubakar Ta Yi Ridda Zuwa Kiristanci Bayan Warkewa Daga Jinyar Shekara Tara

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Jarumar fina-finan Nollywood, Halima Abubakar, ta bayyana cewa ta rungumi addinin Kiristanci bayan ta ce Allah ya warkar da ita daga wata rashin lafiya da ta shafe kusan shekaru tara tana fama da ita.

Halima ta ce ta sha fuskantar barazanar rasa ranta a lokacin jinyar, amma bayan samun lafiya ta yanke shawarar sadaukar da rayuwarta wajen bautar Yesu Almasihu.

Ta ce sauyin da ta samu ba wai na lafiyar jiki kaɗai ba ne, har da sauyin rayuwa ta fuskar addini.

Jarumar ta kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fito fili ta bayar da cikakken shaidar yadda ta ce Allah ya yi amfani da Queen Belemzy Ministries (School of Power) wajen dawo mata da lafiya.

– Wakiliya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img