Na Daina Zuwa Coci Domin Duk Coci da Na Je Ban Samu Natsuwa da Farin Cikin da Nake Nema Ba – AY Makun

DA DUMI-DUMI

Fitaccen ɗan wasan barkwanci kuma jarumi a Najeriya, AY Makun, ya bayyana dalilin da ya sa ya daina halartar ibadar coci, yana mai cewa hakan ba saboda ya daina imani da Allah ba ne, sai dai saboda irin yadda wasu mambobin coci suka riƙa kallonsa bayan labaransa sun bazu a kafafen sada zumunta.

AY Makun ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya ce ya daina zuwa cocinsa na farko saboda ba ya son ya kasance abin raɗe-raɗi da kallon ban mamaki a cikin gidan ibada.

Ya ce daga baya ya fara zuwa wata sabuwar coci, inda aka tarbe shi hannu bibbiyu, har ya gana da fasto, iyalansa da wasu shugabannin cocin, lamarin da ya sa ya yi tunanin ya sami wurin ibada da zai ci gaba da zuwa.

Sai dai AY Makun ya ce bayan an gayyace shi ya shiga wani shiri a cocin, daga bisani aka sanar da shi cewa an cire sunansa saboda fargabar yadda jama’a za su ɗauki matakin idan aka haɗa shi da shirin.

Jarumin ya jaddada cewa ba ya sukar fastoci, illa dai yana son tunatar da coci rawar da ya kamata ta taka wajen karɓar mutane musamman waɗanda ke fuskantar ƙalubale ko suka shiga cece-kuce.

AY Makun ya ce ko da zarge-zargen da ake yi masa gaskiya ne ko ƙarya, coci ita ce ya kamata ta zama mafaka ta gaskiya, gafara da gyaran rayuwa.

Ya ƙara da cewa idan mutum ba zai iya komawa gidan Allah ba lokacin da yake cikin ƙunci, to hakan na nufin ya rasa wurin neman natsuwa da sabuwar dama.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img