Ka Iya Bakin Ka – Dr. Gumi Ya Gargaɗi Gwamna Bago Kan Kalaman da Ya Yi Game da Fulani

DA DUMI-DUMI

Gumi Ya Gargaɗi Gwamna Bago Kan Kalaman da Ya Yi Game da Fulani

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargaɗi Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, da ya riƙa yin taka-tsantsan wajen zaɓen kalamansa yayin magana kan al’amuran Fulani.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, Sheikh Gumi ya ce shugabannin siyasa ya kamata su kasance masu lura da kalamansu, musamman a ƙasa mai cike da mabiya addinai daban-daban, domin kalamai marasa hikima na iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Ya ce, “Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umar Bago, yana buƙatar yin taka-tsantsan wajen zaɓen kalamansa. Yawan surutun siyasa ba ya amfanar shugabanci nagari, musamman a al’umma mai addinai mabambanta.”

Sheikh Gumi ya yi wannan martani ne bayan Gwamna Bago ya gana da shugabannin Fulani, inda ya buƙace su su shawo kan ‘ya’yansu da ke da hannu a garkuwa da mutane da fashi da makami su daina aikata laifuka su koma rayuwa ta gari.

Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa yin shiru da shugabannin al’umma ke yi kan ayyukan masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga na ƙara jawo zargin al’ummar Fulani baki ɗaya.

Haka kuma, Mohammed Umar Bago ya buƙaci shugabannin Fulani su taimaka wajen gano masu aikata laifuka tare da haɗa kai da jami’an tsaro domin magance matsalar rashin tsaro a jihar.

A wani ɓangare na jawabinsa, gwamnan ya umarci sarakunan gargajiya su sanya ido kan wa’azin addini a yankunansu, tare da bayar da umarnin cafke duk wanda ke amfani da wa’azi wajen tunzura rikici tsakanin Musulmi ko tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Ya kuma gargaɗi ƙungiyoyin masu sintiri da kada su ɗauki doka a hannunsu, sannan ya hana noma a bakin hanyoyin gwamnati.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img