Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, gwamnatinsa za ta ƙara nauyin haraji kan masu hannu da shuni domin tallafa wa talakawa da kuma bunƙasa sassan tattalin arziki masu samar da ayyukan yi.
Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Channels Television a ranar Lahadi, inda ya ce gwamnatinsa za ta karkatar da kuɗaɗen da ake rasa ta hanyar rangwamen haraji da ya ce ba a bayyana dalilansu yadda ya kamata ba, zuwa fannoni kamar noma da sauran sassan da za su haɓaka tattalin arziki.
Da aka tambaye shi ko zai ɗora wa masu arziki ƙarin haraji domin tallafa wa marasa ƙarfi, Peter Obi ya amsa da cewa eh, yana mai jaddada cewa masu kuɗi ya kamata su ba da gudunmawa mafi girma wajen ci gaban ƙasa.
Ya ce manufarsa ita ce tabbatar da an yi amfani da albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin inganta rayuwar ‘yan Najeriya da ƙarfafa samar da ayyukan yi.





