Na Biya N1,000 Domin Yin Kashi – Matashi Ya Yi Korafi Kan Kuɗin Gidan Wanka a Kano

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Wani matashi mai suna Mujibu Hamza ya bayyana yadda ya biya N1,000 bayan amfani da wani gidan wanka na jama’a da ke kan titin Magaji Rumfa a jihar Kano.

A cewarsa, bayan ya gama bukatarsa, ya fito ya miƙa N200, yana zaton wannan ne kuɗin amfani da gidan wankan. Sai dai mai kula da wurin ya gaya masa cewa kuɗin shiga gidan wankan N1,000 ne.

Mujibu ya ce ya yi mamakin farashin, inda ya ce har a wasu manyan wurare irin su Bristol Place ba a cajin irin wannan kuɗi saboda amfani da bandaki.

A ƙarshe, ya ce dole ya ƙara N800, ya cika N1,000, sannan cikin barkwanci ya rubuta:

“Lallai yau Mujibu ya yi kashi mai tsada!”

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Wakiliya ba ta samu damar tabbatar da ko wannan ne ainihin kuɗin da ake karɓa a gidan wankan da abin ya faru ba, ko kuma ko akwai wani dalili da ya sa aka karɓi wannan adadi.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img