Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 8.05 Domin Ginawa Da Gyaran Masallatai Da Coci-Coci a Fadin Kasar

Daga Wakiliya

Gwamnatin Tarayya ta ware kimanin Naira biliyan 8.05 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin gina, gyarawa da kuma inganta masallatai da coci-coci a sassa daban-daban na ƙasar nan, duk da cewa kasafin ya nuna gibin kuɗi na Naira tiriliyan 31.45.

Rahoton Tracka, wani shiri na ƙungiyar BudgIT da ke bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati, ya nuna cewa an tanadi kuɗin ne domin aiwatar da ayyuka 59 da suka shafi wuraren ibada.

Daga cikin kuɗin, an ware Naira biliyan 6.14 domin ayyuka 52 da suka shafi masallatai, yayin da aka ware Naira biliyan 1.91 domin ayyuka 7 na coci-coci.

Rahoton ya ce kuɗaɗen za su haɗa da gina sababbin masallatai da coci-coci, gyaran tsofaffi, samar da hasken rana (solar), rijiyoyin burtsatse, kafet, makarantun Islamiyya, shinge da gidajen limamai.

Sai dai binciken ya kuma nuna cewa wasu daga cikin waɗannan ayyukan an ɗora su ne kan hukumomi da ma’aikatun gwamnati waɗanda aikinsu bai shafi gina wuraren ibada ba.

A halin yanzu, kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2026 ya kai kusan Naira tiriliyan 68.3, yayin da aka ware Naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashin ƙasa kaɗai. Bayanai daga Debt Management Office (DMO) kuma sun nuna cewa bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.28 zuwa ƙarshen shekarar 2025.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img