Maza A Yanzu Ba Sa Son Nuna Soyayya Saboda Tsoron a Kira Su ‘Simpawa’ – Tyla

DA DUMI-DUMI

‘Maza A Yanzu Ba Sa Son a Ce Su Masu Tsananin Nuna Soyayya Ne’ — Mawakiya Tyla

Mawakiyar Afirka ta Kudu, Tyla Laura Seethal, wacce aka fi sani da Tyla, ta ce maza da dama a wannan zamani ba sa son bayyana irin soyayyar da suke yi saboda tsoron kada a kira su “basimpe ko simpawa” wato mutumin da ke nuna tsananin kulawa da soyayya ga mace.

Tyla ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa, inda ta ce soyayya ta zama mai wahala saboda yadda wasu maza ke ƙoƙarin ɓoye yadda suke ji.

Ta ce dangantaka mai kyau tana buƙatar daidaito, inda mutum zai san lokacin da ya kamata ya nuna kulawa da kuma lokacin da ya kamata ya rage.

A cewarta, maza da dama yanzu suna jin kunyar nuna ƙauna sosai saboda tsoron abin da mutane za su ce.

Sai dai Tyla ta ƙarfafa maza da kada su ji kunya idan suna son matansu.”

Idan kana son matarka, ka fito ka nuna hakan. Kada ka ji kunya,” in ji ta.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img