Kamfanin hada magunguna na ƙasar Masar, Utopia Pharmaceuticals, ya bayyana shirinsa na gina babbar masana’antar samar da magunguna a Jihar Abia domin biyan buƙatun kasuwar Najeriya da sauran ƙasashen Yammacin Afirka.
Shugaban kamfanin, Kamel Muhamed, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, a garin Nvosi da ke ƙaramar hukumar Isiala Ngwa South.
Kamel Muhamed ya ce kamfanin na neman haɗin gwiwa da gwamnatin jihar domin kafa masana’antar a matsayin wani ɓangare na faɗaɗa ayyukansa a nahiyar Afirka. Ya ce wannan zai taimaka wajen mayar da Najeriya cibiyar fasahar zamani ta samar da magunguna a yankin.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin na aiki ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Masar da NAFDAC kan rajistar magunguna, kuma ya riga ya aiwatar da irin wannan shiri a Tanzaniya da wasu ƙasashen Afirka.
A nasa ɓangaren, Gwamna Alex Otti ya maraba da shirin, yana mai cewa gwamnatinsa ta fi bai wa masana’antun da ke samar da kayayyaki muhimmanci fiye da masu shigo da su daga ƙasashen waje.
Ya ce kafa masana’antar zai samar da ayyukan yi, ya bunƙasa tattalin arziki, ya rage talauci tare da kawo sabbin fasahohi jihar.
Gwamnan ya ba kamfanin tabbacin cikakken goyon bayan gwamnatin jihar, tare da ba da shawarar a kafa masana’antar a yankin Ukwa, saboda yalwar iskar gas, ingantaccen wutar lantarki daga Geometric Power, da kuma wadataccen fili da ya dace da ci gaban masana’antu.




