Manna Firiji da Bango Ka Iya Jawo Ƙarin Cin Wutar Lantarki -inji masana

Me Ya Sa Dole A Bar Tazara Tsakanin Firiji da Bango? Masana Sun Yi Bayani

Daga Wakiliya

Masana sun shawarci masu amfani da firiji da su tabbatar sun bar isasshen tazara tsakanin firiji da bango domin na’urar ta yi aiki yadda ya kamata tare da rage yawan amfani da wutar lantarki.

A cewar masana’antun firiji, tazarar da ya dace ba ɗaya ba ce. Kamfanin LG ya ba da shawarar a bar santimita 10 tsakanin bayan firiji da bango, sannan a bar santimita 30 tsakanin saman firiji da rufi.

Shi kuma Samsung ya ce mafi dacewa shi ne a bar santimita 5 zuwa 7 a kowane gefe na firiji, amma idan sarari ya yi ƙanƙanta, aƙalla santimita 2 zuwa 3 zai iya isa.

Masana sun bayyana cewa wannan tazara tana ba firiji damar fitar da zafi yadda ya kamata. Idan aka matse shi da bango ko kabad ba tare da isasshen sarari ba, hakan na iya sa firiji ya riƙa aiki fiye da kima, ya ƙara cin wutar lantarki, har ma ya rage tsawon rayuwar na’urar.

Saboda haka, ana ba masu siyan sabon firiji shawarar su karanta umarnin da masana’anta suka bayar kafin girkawa, domin kauce wa matsalolin da ka iya tasowa daga rashin barin isasshen tazara tsakanin firiji da bango.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img