Muna Tunkarar Babbar Matsala Idan Har Aka Zura Ido, Najeriya Ta Ci Gaba Da Karɓar Bashi – Aliyu Nuhu
Daga Wakiliya
A yadda muke ci gaba da karɓar bashi, akwai yiwuwar wata rana Najeriya ta kasa biyan bashin da ake bin ta. Ko hakan ya faru a zamanin Bola Tinubu ko bayan ya bar mulki, a wannan lokacin ne za a ga ainihin halayen masu ba mu rance kamar IMF da Bankin Duniya, waɗanda a yanzu suke yabawa waɗannan shirmammun manufofin wannan gwamnati.
Idan Najeriya ta kasa biyan bashin da ake bin ta, abu na farko da masu ba da rancen za su yi shi ne dakatar da ba mu sabon bashi. Saboda shugabanninmu sun saba dogaro da bashi, hakan na iya sa gwamnati ta ƙara haraji a kan al’umma, duk da cewa mutane sun riga sun shiga ƙunci.
Haka kuma, idan ba a samu shigowar daloli ba, darajar Naira za ta ƙara faɗuwa. Tuni Naira ta yi asarar darajarta sosai bayan tsarin canjin kuɗi ya zama a bude. Idan hakan ya ci gaba, masu zuba jari za su fice da kuɗinsu, abin da zai ƙara jefa tattalin arzikin ƙasa cikin matsala.
Sakamakon haka, kayan da ake shigowa da su daga ƙasashen waje kamar abinci, mai da magunguna za su yi tsada sosai, wasu ma su yi ƙaranci. Haka kuma, duk wanda ya ajiye kuɗinsa a Naira zai ga darajar kuɗinsa ta ragu sosan gaske.
Wannan barazana tana da yiwuwar faruwa domin mafi yawan kuɗin da Najeriya ke biyan bashi da su suna fitowa ne daga man fetur, wanda farashinsa kan riƙa sauyawa saboda abubuwan da ba ƙasar ke da iko a kansu ba.
Gwamnati mai hangen nesa ba za ta dogara da bashi ba. Maimakon haka, tana rage almubazzaranci, tana tanadin kuɗi domin gaba, tana zuba jari a ilimi, lafiya da manyan ayyukan raya ƙasa.
Marubucin ya yabawa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, inda ya ce ya tattara ƙwararrun masana tattalin arziki, ya biya bashin Najeriya, kuma ya guji ci gaba da karɓar bashi. Obasanjo ya karɓi ragamar mulki lokacin da ajiyar kuɗin waje ta Najeriya ke kusan dala biliyan 4.99, amma ya bar ta tana da kusan dala biliyan 43.77 tare da rage nauyin bashi. Haka kuma ya kafa Dokar Kula da Harkokin Kuɗaɗen Gwamnati (Fiscal Responsibility Act), wadda ta tanadi cewa a riƙa karɓar bashi ne kawai domin manyan ayyukan raya ƙasa da bunƙasa rayuwar jama’a.
Amma ga dukkan alamu ana zargin wannan Gamnati ta Bola Tinubu da Majalisar Dokoki na ci gaba da karɓar bashi domin abubuwan da ba su da muhimmanci, wanda hakan na iya jefa Najeriya cikin mawuyacin hali nan gaba.
Muna addu’ar Allah Ya albarkaci shugabanni na gari irin Olusegun Obasanjo.
Fassarar sharhin Aliyu Nuhu.




