Ku goyi bayan Tinubu da Shettima saboda addininku – Matawalle

DA DUMI-DUMI

‘Ku goyi bayan Tinubu da Shettima saboda addininku; Ku Shahidai ne, ko mutuwa kuka yi wajen tabbatar da nasararsu, kuna sa ran rahamar Allah’ — Matawalle

Daga Wakiliya

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya roƙi matan Musulmi a Najeriya da su goyi bayan takarar Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a zaɓen 2027.

Matawalle ya yi wannan kira ne a wani taron siyasa da aka gudanar a Kaduna, inda ya bayyana cewa goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi ya samo asali ne daga imanin mutum

Ya ce bai kamata su damu da masu sukar matsayinsu ba, domin suna yin hakan ne saboda addininsu da kuma neman yardar Allah. Ku shahidaine, ko mutuwa kuka yi a wajen tabbatar da nasarar Tinubu da Shettima kuna sa ran samun rahamar Allah – inji Matawalle

A wajen taron, tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Masari, ya ce a cikin kusan shekaru 40 da ya shafe yana siyasa, bai taɓa ganin shugaban ƙasa mai tsare-tsare irin na Bola Tinubu ba.

Matawalle da Masari na cikin kwamitin yakin neman zaɓen Shugaba Tinubu na jam’iyyar APC na shekarar 2027.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img