“Har yanzu farashin man fetur a Najeriya ya fi na wasu ƙasashen waje sauƙi” – Ministan Mai

DA DUMI-DUMI

“Har yanzu farashin man fetur a Najeriya ya fi na wasu ƙasashen waje sauƙi” – Ministan Mai

Daga Wakiliya

Ministan Ƙasa na Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun fara amfana da cire tallafin man fetur da kuma tace man a cikin gida.

Lokpobiri ya ce gwamnati ba ta da ikon kayyade farashin man fetur saboda an yi cikakken tsarin sassaucin farashi, wanda ya danganta farashin da yanayin kasuwar duniya.

Ya ce ko da yake ana tace man fetur a Najeriya, har yanzu ɗanyen mai ana sayar da shi bisa farashin kasuwar duniya, don haka hakan ba ya nufin dole farashin fetur ya yi sauƙi.

Ministan ya ce matsakaicin farashin fetur a Najeriya ya kasance ƙasa da na Amurka, inda ya bayyana cewa lita ɗaya a Najeriya tana kusan N1,430, yayin da a Amurka take kusan N1,633.

Lokpobiri ya ce dawo da tallafin man fetur ne kaɗai zai bai wa gwamnati damar shiga tsakani kai tsaye wajen rage farashin.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img