An nemi babban soja ya biya N50m ko a kashe shi, daga baya aka gano ashe orderly dinsa ne
Daga Wakiliya
An zargi wani ma’aikacin kusa da wani babban jami’in soja da hannu wajen aika masa da sakonnin barazanar kashe shi, tare da neman ya biya Naira miliyan 50.
Lauya, Barrister Hamza Dantani, ne ya bayyana lamarin, inda ya ce jami’in sojan ya shafe kwanaki yana karɓar sakonnin barazana.
A cewar Dantani, masu barazanar sun yi ikirarin cewa sun san harkokin jami’in da kuma inda yake yawan zuwa, sannan suka ce idan bai biya N50m ba, za su kashe shi.
Daga baya jami’in ya amince zai biya N20m, amma ya nemi a tura masa da lambar asusun da zai aika kudin.
Bayan an turo masa da asusun, sai jami’in ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda a Abuja.
Binciken ’yan sandan ya nuna cewa asusun na wani ɗan canji ne da ke aiki a Zone 4, Abuja.
A lokacin da aka gayyaci ɗan canjin, ya bayyana cewa wani soja ne da ya saba zuwa wurinsa don canjin kuɗi ya ba shi umarnin tura asusun.
Daga baya binciken ya kai ga zargin cewa wanda ke da hannu wajen shirya aika sakonnin barazanar ba wani ba ne, face orderly, wato ma’aikacin da ke kusa da babban sojan kuma yake yi masa hidima a kullum.
Lamarin ya haifar da tambayoyi kan yadda wani mutum da aka ba amanar kula da jami’i zai iya shiga cikin shirya masa barazana.




