Kirista da mai bautar gargajiya na iya neman auren ɗiya ta -inji fitaccen Malamin Musulunci

DA DUMI-DUMI

Kiristoci da masu bautar gargajiya na iya neman auren ‘yata idan suna da hali nagari – Malamin Musulunci TAOSAF

Shahararren malamin Musulunci, Taoheed Abdulwasiu Mustapha (TAOSAF), ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ya bayyana cewa Kiristoci da masu bin addinan gargajiya na iya neman auren ‘yarsa, muddin suna da kyawawan halaye kuma suna da halalacciyar hanyar samun abin rayuwa.

A cikin wani saƙo da ya wallafa, TAOSAF ya ce shi Musulmi ne, amma yana ɗora darajar ɗan Adam da mutunci a gaba.

Ya ce duk wanda ya fito daga gida nagari, yana da kyawawan ɗabi’u kuma yana da abin dogaro na halal, zai girmama shi kuma ba zai hana shi neman auren ‘yarsa ba saboda bambancin addini.

Malamin ya kuma bayyana cewa ba ya goyon bayan duk wata fahimtar addini da ke koyar da ƙiyayya ko nuna wariya ga mutane saboda bambancin addini.

Sai dai kalamansa sun haddasa muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, inda wasu suka yaba da kiran zaman lafiya da haƙuri tsakanin mabiya addinai, yayin da wasu kuma suka nuna rashin amincewarsu da ra’ayin.

Wakiliya ta lura cewa batun ya ci gaba da jan hankalin jama’a, musamman kan batun aure tsakanin mabiya addinai daban-daban da kuma zaman tare cikin mutunta juna.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img