Tinubu Zai Lashe Arewa a 2027 Don Mutane Ba Za Su Yi Zaɓe Bisa Addini Ko Ƙabila Ba – inji Uba Sani

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu gagarumar nasara a Arewacin Najeriya a zaɓen shekarar 2027.

A wata hira da ya yi da Arise News, Uba Sani ya ce al’ummar Arewa ba za su yi zaɓe bisa addini, ƙabila ko yanki ba, sai dai bisa abin da suke ganin ya dace.

Ya kuma soki masu cewa zaɓen 2027 zai kasance tsakanin jam’iyyar APC da al’ummar Najeriya, yana mai cewa wannan hujja ce mai rauni.

“Tinubu zai yi nasara a Arewa a 2027. Mutanen Arewa ba za su yi zaɓe bisa addini, ƙabila ko yanki ba. Kuma masu cewa zaɓen zai kasance tsakanin APC da al’ummar Najeriya suna gabatar da hujja mafi rauni da na taɓa ji,” in ji shi.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img