A daina sukar bashin da Tinubu ke karbowa a dubi abin da ake yi da kuɗin -inji Ministan Kudi
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce sukar bashin da gwamnati ke ci ba tare da la’akari da dalilin aro, farashinsa da ribar da zai haifar ba, ba hanya ce mai amfani ba.
Da yake jawabi a taron Capital Market Academics of Nigeria (CMAN) a Abuja ranar Talata, Oyedele ya ce abin da ya kamata a tambaya shi ne ko an yi amfani da bashin wajen samar da ayyuka da ci gaban da zai zarce kuɗin ruwa da za a biya.
Ya ce Najeriya ta ɗauki bashi a matsayin abin kunya maimakon kayan aikin bunƙasa tattalin arziki, yana mai cewa idan aka tsara shi yadda ya dace, bashi na iya hanzarta ci gaba maimakon zama matsala.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da su rungumi tsarin haɗa jari (equity) maimakon nacewa mallakar kashi 100 cikin 100 na ƙananan kamfanoni, yana mai cewa hakan zai ba su damar faɗaɗa kasuwancinsu.
Oyedele ya ƙara da cewa Najeriya na buƙatar inganta amincewar masu zuba jari ta hanyar tabbatar da daidaiton manufofi, kare kwangiloli da kuma kafa kotun musamman da za ta rika warware rikice-rikicen kasuwanci cikin gaggawa.
Ya kuma bayyana cewa gibin kuɗaɗen da ƙananan da matsakaitan sana’o’i (MSMEs) ke buƙata ya haura dala biliyan 200, yana mai kira da a samar da sabbin hanyoyin samun jari domin bunƙasa kasuwanci.





