Gwamnatin Tinubu ta aika da murhun girki 3,400 domin a raba wa mata a Kano
Daga Wakiliya
Gwamnatin Kano ta fara rabon murhun girki guda 3,400 da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta bai wa jihar, domin rabawa mata masu karamin karfi.
Kwamishinan Muhalli, Ruwa da Sauyin Yanayi na jihar, Dahir M. Hashim, ya jagoranci fara rabon murhun a ranar Lahadi, inda aka rabawa mata 800 a matakin farko.
Kwamishinan ya ce amfani da itacen girki na jefa mata cikin hadarin kamuwa da cututtukan numfashi sakamakon shakar hayaki na tsawon lokaci.




