California ta amince da bukukuwan Idi a matsayin ranakun hutu

DA DUMI-DUMI

A hukumance jihar California ta Amurka ta amince da bukukuwan Idi a matsayin ranakun hutu

Daga Wakiliya

Jihar California da ke Amurka ta amince da karamar sallah da babbar sallar idi, wato Eid al-Fitr da Eid al-Adha a matsayin ranakun hutu da jihar ta amince da su a hukumance.

Gwamna Gavin Newsom ya rattaba hannu kan dokar Assembly Bill 2017, wadda ta sanya ranar farko ta watan Shawwal da ranar 10 ga watan Dhul-Hijjah cikin jerin ranakun da jihar ta amince da su.

California ce jiha ta biyu a Amurka da ta dauki irin wannan mataki, bayan Washington da ta amince da bukukuwan a shekarar 2025.

Sabuwar dokar ta bai wa ma’aikatan jihar damar amfani da hutun da suke da shi domin gudanar da bukukuwan, yayin da makarantu za su iya rufe ko ba wa dalibai hutun idan dokokin yankinsu sun amince.

Sai dai kotunan jihar ba za su rufe ba a ranakun bukukuwan.

Eid al-Fitr na nuna karshen azumin watan Ramadan, yayin da Eid al-Adha ke tunawa da biyayyar Annabi Ibrahim ga Allah s.w.t

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img