Adeyanju ya zargi Tinubu da “yin wasan kwaikwayo” kan rashin lafiyarsa don yaudarar yan Najeriya
Daga Wakiliya
Dan gwagwarmayar siyasa kuma mai sharhi kan al’amuran Najeriya, Deji Adeyanju, ya yi zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da wata matsalar rashin lafiya, yana mai cewa bai kamata ‘yan Najeriya su sake yarda da abin da ya kira “wasan kwaikwayo” ba.
Adeyanju ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su sake fadawa abin da ya ce ya faru a lokacin yakin neman zaben 2023.
Ya ce: “Kada a sake yaudararku da wasannin Tinubu karo na biyu. Ba shi da lafiya. Haka ya kasance yana nuna kamar ba shi da lafiya kuma yana fadin maganganu marasa ma’ana a shekarar 2023 domin samun kuri’u, bayan zabe kuma ya koma kamar komai bai faru ba, yana magana da manyan kalmomi na turanci”
Adeyanju ya kara cewa wadanda suka yarda da irin wannan yanayi a karo na biyu, su ne za su dauki nauyin abin da ya faru.
Sai dai, zarge-zargen da suka shafi lafiyar Tinubu sun kasance batun ce-ce-ku-ce tun kafin zaben 2023. A lokacin, Tinubu da masu goyon bayansa sun musanta cewa yana fama da wata babbar rashin lafiya.




