Daga Wakiliya
Fitaccen jarumin fina-finan faɗa na duniya, Jackie Chan, zai sake dawo wa masoyansa da irin hatsabibiyar kasadar da ya shahara da ita a tsofaffin fina-finansa, yayin da ake shirye-shiryen samar da sabon fim ɗinsa mai suna Armour of God IV: Ultimatum.
Ko da yake Jackie Chan na da shekaru 72, hotunan da aka fitar daga bayan fagen shirya fim ɗin sun nuna cewa har yanzu yana shirin yin manyan abubuwan kasada da suka kasance alamarsa tun farkon aikinsa.
Sabon fim ɗin zai ci gaba da labarin Asian Hawk, jarumin da Jackie Chan ke takawa, wanda zai sake shiga wata gagarumar kasada domin neman wani tsohon kayan tarihi mai suna Tumar, wanda aka ɗora ladan sama da dala miliyan 20 ga duk wanda ya gano shi.
An fara jerin fina-finan Armour of God ne a shekarar 1986, sannan aka fitar da Operation Condor a 1991 da kuma CZ12 (Chinese Zodiac) a 2012. Yanzu kuwa, bayan fiye da shekaru 40, Jackie Chan zai sake dawo da wannan shahararren jerin fina-finai.
Rahotanni sun ce za a fara ɗaukar Armour of God IV: Ultimatum a ƙasar Kazakhstan a bazarar shekarar 2026, yayin da ake sa ran za a saki fim ɗin a faɗin duniya a shekarar 2027.





