Jami’an kashe gobara a Amurka sun ceci wata kurciya da ta shaƙi hayaƙi a gobara

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Jami’an kashe gobara a birnin Oakland na ƙasar Amurka sun ceci wata kurciya da ta shaƙi hayaƙi bayan gobarar da ta tashi a wata mota.

Bayan sun kashe gobarar, jami’an sun hango kurciyar tana fama da wahalar numfashi, inda ta ƙaraso kusa da su kamar tana neman taimako.

Kungiyar Oakland Firefighters Local 55 ta ce jami’an sun ba kurciyar iskar oxygen, kuma bayan ta samu sauƙi ta kuma fitar da hayaƙin da ya shiga huhu, sai ta tashi ta ci gaba da tafiyarta.

Lamarin ya ja hankalin mutane da dama, inda aka yaba wa jami’an saboda tausayi da kulawar da suka nuna, ba ga mutane kaɗai ba har da dabbobi.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img