Ireland Ta Buɗe Tallafin Ƙaro Karatu Kyauta Ga ‘Yan Najeriya Da Ghana

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Ofishin Jakadancin Ireland da ke Najeriya ya sanar da buɗe neman guraben karatun digiri na biyu (Master’s) na shekarar 2026 ƙarƙashin shirin Ireland Fellows Programme, wanda ke ba ɗalibai cikakken tallafin karatu a ƙasar Ireland.

A cewar ofishin jakadancin, za a fara karɓar buƙatun ne daga 29 ga Yuni zuwa 26 ga Yuli, 2026, kuma shirin ya shafi ƙwararrun ma’aikata na matakin farko da matsakaici daga Najeriya da Ghana.

Tallafin ya haɗa da biyan kuɗin makaranta, kuɗin rayuwa na wata-wata, masauki, kuɗin tafiya da biza, da kuma inshorar lafiya.

Domin cancanta, dole ne mai neman gurbin ya kasance ɗan ƙasar Najeriya ko Ghana, yana zaune a ƙasarsa, ya mallaki digiri na farko da aƙalla Second Class Lower, sannan ya samu aƙalla shekaru uku na ƙwarewar aiki.

Haka kuma, ga ‘yan Najeriya akwai Roger Casement Fellowship in Human Rights, wanda ke tallafa wa masu son yin karatu a fannonin Shari’a, Haƙƙin Dan Adam da Mulki Nagari.

Ana gabatar da dukkan buƙatun ne ta yanar gizo ta shafin hukuma na Ireland Fellows Programme.

Masu bukata na iya shiga ta wannan shafi da ofishin ya bayyana https://irelandfellows.africa @commercium_afr

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img