RA’AYI: Ana Zargin Babachir ne ya fi haddasa rikicin da ya raunana jam’iyyar ADC kafin shima a karshe ya fice ya bar ta

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Ana zargin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, shi ne ya fi haddasa rikicin da ya raunana ADC kafin a karshe shi ma ya fice daga jam’iyyar bayan ya gama lalata ta.

A cewar masu wannan zargi:

– Yaƙin cikin gida ya sa Bindow ya fice.
– Ishaku Abbo ya fice.
– Aishatu Binani ta fice.
– Nyako ya fice.
– Rikicin shari’ar Nafiu Bala ya ƙara dagula al’amura, amma kuma ana zargin duk Babachir ne sila!

Abun takaici kuma bayan ya kunna waɗannan rikice-rikice da ake zargi, Babachir din shi ma ya fice daga ADC, lamarin da ya bar Atiku Abubakar kusan shi kaɗai ne jigon haɗakar,


…sai dai ya sha musanta hakan har ma yana zargin shi ake yiwa rashin adalci a jam’iyyar sannan babu wata hujja a fili da ta tabbatar cewa Babachir ne kai tsaye ya haddasa ficewar waɗannan mutane, domin kowane ɗayansu na iya kasancewa yana da nasa boyayyen dalilai na siyasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img