Tinubu Ya Kafa Ofishin Da Zai Rika Tattara Bayanai Kan Kiwon Lafiyar Yan Najeriya

DA DUMI-DUMI

TINUBU YA KAFAR DA SABON OFISHI DON INGANTA AMFANI DA FASAHA DA BAYANAN LAFIYA, YA NAƊA OBI ADIGWE A MATSAYIN SHUGABA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Ofishin Fasahar Lafiya da Nazarin Bayanai na Ƙasa (NHTDAO) domin inganta yadda ake amfani da fasahar zamani da tattara bayanan lafiya a Najeriya.

Haka kuma, shugaban ya naɗa Obi Adigwe a matsayin shugaban farko na ofishin.

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, sabon ofishin zai haɗa dukkan tsarin bayanan lafiya na gwamnati da masu zaman kansu, domin asibitoci da cibiyoyin lafiya su riƙa aiki da tsari guda, cikin sauƙi da tsaro.

Me hakan ke nufi ga ‘yan Najeriya?

Sabon ofishin zai taimaka wajen amfani da bayanan lafiya ta hanyar zamani, wanda ake sa ran zai:

– Inganta yadda ake kula da marasa lafiya.
– Sauƙaƙa adana da musayar bayanan lafiya tsakanin asibitoci.
– Taimaka wa gwamnati wajen yanke shawara bisa ingantattun bayanai.
– Ƙarfafa amfani da fasahar zamani da bayanai wajen bunƙasa harkar lafiya.

An ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Tinubu na inganta tsarin kiwon lafiya da amfani da fasahar zamani a faɗin ƙasar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img