“Idan Ba Ku Kiyaye Ni Ba, Zan Yi Tone-Tone” – Mansura Isa ta Gargaɗi Rarara da Matarsa bayan ya nemi ta zaɓi Shi Ko Seyi Tinubu

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Mansura Isa Ta Zargi Rarara da Danniya, Ta Ce Ya Nemi Ta Zaɓi Tsakaninsa da Seyi Tinubu

Fitacciyar jarumar Kannywood, Mansura Isa, ta caccaki mawaki Dauda Kahutu Rarara da matarsa, Aisha Humaira, inda ta zarge su da amfani da mutane wajen cimma muradun siyasa ba tare da ba su amfanin da ya dace ba.

A cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa, Mansura Isa ta ce Rarara ya taba bukatar ta zabi tsakaninsa da ɗan Shugaban Ƙasa, Seyi Tinubu. Ta ce ta zabi bin tafiyar Seyi Tinubu, lamarin da ya sa ta fice daga tafiyar mawakin.

Jarumar ta kuma yi zargin cewa Rarara na son komai ya rika bi ta hannunsa, yana kuma kokarin mamaye harkokin da suka shafi goyon bayan siyasa. A cewarta, kowane mutum na da ‘yancin zabar wanda zai mara baya ko kuma kada ya mara masa baya.

Mansura Isa ta ce ko mutum ya goyi bayan gwamnati ko bai goyi bayanta ba, yana da hakkin cin moriyar ƙasa a matsayinsa na ɗan ƙasa, domin gwamnati ta kowa ce.

Ta kuma yi gargadin cewa a daina yi mata kutse ko shirya mata makirci, tana mai cewa idan hakan ya ci gaba za ta bayyana wasu bayanan da ta ce ba za su yi wa wasu daɗi ba.

Zarge-zargen da Mansura Isa ta yi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jin irin korafe-korafen da wasu ke yi kan cewa Dauda Kahutu Rarara na amfani da mutane wajen samun damar siyasa da kuɗi, amma ba ya ba su isasshen sakamako.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Dauda Kahutu Rarara bai fitar da wata sanarwa ko martani kan zarge-zargen ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img