Bude Ofishin bogi irin PFIPC ba sabon abu bane, An taɓa samun irinsa a mulkin Buhari – ACF

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta yi zargin cewa irin ofishin da ake kira Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) ya taɓa wanzuwa a zamanin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, sai dai daga baya aka sake masa fasali ta hanyar ƙara kalmar “Presidential”.

Mai magana da yawun ACF, Farfesa Tukur Baba, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar Arise Television ranar Asabar.

A cewarsa, akwai mutanen da ke cikin gwamnati da suka san yadda tsarin gwamnati ke aiki, lamarin da ke ba su damar ƙirƙirar irin waɗannan ofisoshi ta hanyoyin da ba su dace ba.

Farfesa Tukur Baba ya kuma tambayi ko an taɓa gabatar da kasafin kuɗin ofishin domin tantancewa, yana mai cewa idan hakan ya faru, me ya sa ba a gano tun da wuri cewa akwai matsala ba.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan cece-ku-ce kan PFIPC, wani ofishi da Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ba ta da masaniya a kansa, tare da bayyana shi a matsayin na bogi.

A baya dai, shugaban PFIPC da ake zargi ya tsere, Adeniyi Adeyemi, ya yi ikirarin cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya karɓi Naira miliyan 400 ta hannun wani wakili, tare da neman ƙarin Naira miliyan 200 domin tabbatar da naɗinsa. Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin baki ɗaya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img