Attajiran Najeriya su riƙa taimaka wa talakawa nauyin da ke kan gwamnati ya yi yawa – Remi Tinubu

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Kada Ku Ƙare Kuɗin Ku Kan Motoci Kaɗai, Ku Taimaki Talakawa – Remi Tinubu Ta Faɗa wa Burna Boy, Davido da Asake

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta buƙaci fitattun mawakan Najeriya da suka haɗa da Burna Boy, Davido da Asake da su kafa gidauniyoyin tallafa wa mabukata tare da amfani da wani ɓangare na arzikinsu wajen rage talauci.

Remi Tinubu ta yi wannan kira ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da National Community Food Bank a Jihar Kogi, inda ta ce duk da cewa mallakar motocin alfarma kamar Maybach da Rolls-Royce ba laifi ba ne, amma ya dace attajirai su taimaka wa talakawa domin nauyin da ke kan gwamnati ya yi yawa.

Ta bayyana mawaƙin Senegal-Amurka, Akon, a matsayin abin koyi saboda ayyukan jin ƙai da yake yi, tana mai kira ga mawakan Najeriya su bi sawunsa ta hanyar kafa gidauniyoyi ko faɗaɗa ayyukan agaji.

Haka kuma, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta jaddada cewa ƙananan sana’o’i kamar sayar da barkono, kayan lambu, gyaɗa, ƙuli-ƙuli da ƙosai na iya zama hanyar samun abin dogaro.

A cewarta, wani matashin da ya kammala jami’a a Abuja wanda ya fara sana’ar sayar da ƙosai bayan ya rasa aiki, ya samu tallafi, kuma yanzu yana ɗaukar ma’aikata 12 yana gudanar da kasuwancinsa cikin nasara.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img