Hotunan Aisha Buhari, Seyi Tinubu, Dino Melaye da wasu jiga-jigan Najeriya tare a Spain ya jawo ce-ce-ku-ce

DA DUMI-DUMI

Hotunan Aisha Buhari, Seyi Tinubu, Dino Melaye da wasu jiga-jigan Najeriya tare a Spain ya jawo ce-ce-ku-ce

Daga Wakiliya

Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, da ɗan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Seyi Tinubu, na cikin fitattun ’yan Najeriya da aka gani tare a wani ƙayataccen wajen shaƙatawa sun haɗu domin taron share fagen bikin aure a Marbella, kasar Spain.

Haka kuma an ga tsohon Sanata Dino Melaye, ɗan kasuwa Ben Murray-Bruce da Terry Waya a wajen taron.

An shirya taron ne a matsayin wani ɓangare na bukukuwan auren Saraya Danjuma, ’yar tsohon Shugaban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Theophilus Danjuma, da angonta Bawa Salaka.

An gudanar da liyafar maraba da baƙi a La Cabane, wani wurin shakatawa na Dolce & Gabbana da ke Marbella, a yankin Málaga na Spain.

Bidiyo da hotunan taron da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna Aisha Buhari, Seyi Tinubu, Dino Melaye da sauran baƙi cikin yanayi na nishaɗi da cuɗanya.

Ganinsu tare ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman saboda wasu daga cikin mutanen suna da alaƙa da bangarorin siyasa daban-daban.

Wasu daga cikin masu amfani da kafafen sada zumunta sun tambayi yadda manyan ’yan siyasar da ke nuna bambancin ra’ayi a bainar jama’a suke taruwa a wajen bukukuwa irin wannan.

Wasu kuma sun ce kasancewar mutanen tare a wani taron aure ba lallai ne ya nuna cewa sun cimma wata yarjejeniya ta siyasa ko kuma suna aiki tare ba.

Rahotanni sun ce bikin auren Saraya Danjuma da Bawa Salaka ya fara ne da shagulgulan gargajiya a Najeriya, kafin a ci gaba da bukukuwan a Marbella.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Tinubu ya yi wa Arewa ayyukan da ba a samu irinsu ba cikin shekaru 40 – don haka mara masa baya a 2027 ya...

“Na yi imani kashi 100 cikin 100 cewa hanyar da ta dace da Arewa ita ce mu ci gaba da goyon bayan Bola Ahmed Tinubu har ya kammala wa’adinsa.”
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img