NiHSA, ta yi gargadin cewa jihohi 15 ciki har da Kogi, Taraba, Benue da Lagos na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa nan da kwanaki bakwai masu zuwa
Daga Wakiliya
Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya, NiHSA, ta yi gargadin cewa jihohi 15 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a cikin kwanaki bakwai masu zuwa.
Hukumar ta ce hasashen ya shafi tsakanin 19 zuwa 25 ga Satumba 2026, inda ta bukaci al’ummomin da ke zaune a wuraren da ke fama da ambaliya su koma wuraren da suke sama da matakin ruwa.
Daraktan-Janar na NiHSA, Arch Umar Mohammed, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar gargadin ambaliyar ruwa da hukumar ta fitar ranar Asabar.
Ya ce ana sa ran tashin ruwan koguna zai haddasa ambaliya a wasu garuruwa, lamarin da ka iya shafar makarantu, asibitoci, kasuwanni, gonaki da wuraren ibada.
Arch Umar Mohammed ya ce jihohin Imo, Cross River, Ebonyi, Benue, Anambra, Akwa Ibom, Edo, Bayelsa, Enugu, Kogi, Delta, Abia, Taraba, Rivers da Lagos na cikin wadanda ke fuskantar hadarin.
A Jihar Imo, NiHSA ta ce kananan hukumomin Aboh-Mbaise, Ahiazu-Mbaise, Ehime Mbano, Ezinihitte, Ideato North, Ihitte/Uboma da Ikeduru ne ke cikin hadarin.
A Cross River kuwa, kananan hukumomin Abi, Akamkpa, Akpabuyo, Biase, Calabar, Calabar South, Ikom da Obubra ne abin ya shafa.
Hukumar ta kuma ce tashoshin ruwa na Obubra, Itigidi da Epento a Cross River na daga cikin wuraren da ake sa ran za a samu karin matakin ruwa.
A Ebonyi, kananan hukumomi shida ne abin ya shafa, yayin da a Benue kananan hukumomin Buruku, Gboko, Guma, Katsina-Ala, Logo da Ukum ke cikin yankunan da aka yi wa gargadin.
NiHSA ta bukaci gwamnatocin jihohin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa wajen kwashe mutanen da ke zaune a wuraren da ambaliyar ka iya shafa zuwa wuraren da suka fi aminci.
Hukumar ta kuma shawarci al’ummomin da ke zaune a filayen da ruwa ke taruwa da su kasance cikin shirin kaura zuwa wuraren da suka fi tsawo.




