Tinubu ya yi wa Arewa ayyukan da ba a samu irinsu ba cikin shekaru 40 – don haka mara masa baya a 2027 ya zama wajibi – Uba Sani
Daga Wakiliya
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya yi kira ga al’ummar Arewa da su ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyukan da ba a samu irinsu ba cikin shekaru 40.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taro da malaman addinin Musulunci da sauran masu ruwa da tsaki suka gudanar a Kaduna.
Gwamnan ya ce, ya kamata shugabannin siyasa da malaman addini a Arewa su yi haƙuri, su kuma faɗi gaskiya kan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta cimma.
Ya ce: “Na yi imani kashi 100 cikin 100 cewa hanyar da ta dace da Arewa ita ce mu ci gaba da goyon bayan Bola Ahmed Tinubu har ya kammala wa’adinsa.”
Hanyar Birnin Gwari
Gwamnan ya kawo aikin hanyar Mando zuwa Birnin Gwari a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan da ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar.
A cewarsa, al’ummar yankin sun shafe kusan shekaru 40 suna neman a gyara hanyar, amma babu gwamnatin da ta kammala aikin.
Ya ce Tinubu ya ware naira biliyan 178 domin sake gina hanyar.
Uba Sani ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta ware naira biliyan 600 domin kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda ya ce ta shafe shekaru ana yin alkawarin gyaranta ba tare da kammalawa ba.
“Tsaro ya inganta”
Gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya inganta sosai.
Ya ce a baya matafiya kan ji tsoron amfani da hanyar, amma yanzu mutane na iya yin tafiya daga Kaduna zuwa Abuja cikin dare.
“Wanda yake tafiya daga Kaduna zuwa Abuja a da sai ya yi addu’ar ƙarshe kafin ya isa Abuja. Amma yau za ka iya tashi bayan sallar Isha’i ka shiga hanya,” in ji shi.
Uba Sani ya ce malaman addini suna da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a, musamman wajen bayyana halin da ake ciki a fannin tsaro, ilimi, lafiya da ayyukan raya ƙasa.
Ya kuma soki wasu daga cikin ’yan siyasar Arewa da yake cewa suna amfani da kalmar “ajandar Arewa” ne domin neman mulki.
Gwamnan ya bukaci malaman da su riƙa faɗin gaskiya tare da tsoron Allah wajen bayyana ci gaban da yake cewa gwamnatin Tinubu ta samu a Arewa.




