Atiku ya ce zai hada kai da kungiyar ‘Tinubu Must Go’ domin kayar da APC a 2027

DA DUMI-DUMI

Atiku ya ce zai hada kai da kungiyar ‘Tinubu Must Go’ domin kayar da APC a 2027

Daga Wakiliya

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce ya amince da tafiyar Tinubu Must Go (TMG), bayan ganawa da daya daga cikin manyan jagororinta, Barrista Abba Hikima.

A wata sanarwa da Atiku ya fitar, ya ce ya karbi bakuncin Abba Hikima, bayan kammala wani zaben intanet da kungiyar ta shirya, wanda ya samu kuri’un mutane dubu 109,799.

Atiku ya ce tikitin sa na ADC tare da Rotimi Amaechi ya samu kashi 73.6 cikin 100 na kuri’un, wato kuri’u 80,809.

Ya ce abin da ya fi muhimmanci a sakamakon zaben shi ne yadda ya nuna, a cewarsa, sha’awar wasu ‘yan Najeriya na ganin an samu sauyi a kasar.

Atiku ya kuma bayyana cewa ya amince da kungiyar TMG, tare da kira ga ‘yan Najeriya masu ra’ayin sauyi da su shiga tafiyar.

Ya ce yana sa ran kara tattaunawa da shugabannin kungiyar domin hada kai wajen cimma burin gina Najeriya mai hadin kai, ci gaba da dimokuradiyya.

Sai dai rahotannin kafafen yada labarai sun nuna cewa zaben na TMG zaben intanet ne na sa’o’i 24, ba zaben kasa ko binciken ra’ayin jama’a na kimiyya da ya wakilci dukkan masu kada kuri’a a Najeriya ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img