Gwamnatin Tarayya Za Ta Horas da Matasa 5,000 Aikin Saka Mitocin Wutar Lantarki a Faɗin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin Power Force Programme ƙarƙashin Presidential Metering Initiative (PMI) domin horas da matasa 5,000 a matsayin ƙwararrun masu girka mitocin wutar lantarki a faɗin Najeriya.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana yayin ƙaddamar da shirin a ranar Alhamis cewa matakin zai taimaka wajen rage ƙarancin mitoci, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma inganta tsarin wutar lantarki a ƙasar.

Joseph Tegbe ya ce rashin isassun mitoci na daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban ɓangaren wutar lantarki, yana mai jaddada cewa idan ba a auna yawan wutar da aka yi amfani da ita yadda ya kamata ba, ba za a iya tara kuɗin da ya dace ba, lamarin da ke hana zuba jari da inganta ayyuka.

Ya ce manufar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ita ce tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya yana biyan kuɗin wutar da ya yi amfani da ita kawai, yayin da kamfanonin samar da wuta su ma suke karɓar kuɗin wutar da suka samar.

A cewarsa, amfani da mitoci na zamani zai rage tsarin ƙiyasin kuɗin wuta (estimated billing), ya rage saɓani tsakanin masu amfani da wuta da kamfanonin rarraba wuta, tare da ƙara gaskiya da amincewar jama’a ga ɓangaren wutar lantarki.

Joseph Tegbe ya kuma yabawa Association of Meter Asset Providers of Nigeria (AMMON) bisa janye ƙarar da ta shafi shirin samar da mitoci, yana mai cewa hakan zai hanzarta rabon mitoci a faɗin ƙasar. Ya bayyana cewa matasan da za a horas za su zama ginshiƙin aikin girka mitocin zamani a Najeriya, tare da tabbatar da cewa gidaje da kasuwanci miliyoyi sun samu mitoci da aka girka bisa ƙa’idodin fasaha da tsaro.

Ministan ya buƙaci waɗanda suka shiga kashi na farko na shirin su yi amfani da damar wajen koyon sana’ar yadda ya kamata, yana mai cewa ƙwarewar da za su samu za ta buɗe musu ƙofofin ayyukan yi tare da taimakawa bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

A ƙarshe, Joseph Tegbe ya bayyana shirin a hukumance a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na gina ingantaccen, gaskiya da dorewar tsarin wutar lantarki domin amfanin ‘yan Najeriya.

DA DUMI-DUMI

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 – Nentawe Yilwatda

APC Za Ta Yi Amfani da Cikakken Ƙarfinta Domin Lashe Zaɓen 2027 Daga Kan Shugaban Kasa Har Kansila - Nentawe Yilwatda

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Kanun Labarai

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img