Ana Take Hakkin Dan Adam a Borno, Musamman Matasa da ‘Ya’yan Talakawa – Barrista Hamza Dantani

DA DUMI-DUMI

Barrista Hamza Nuhu Dantani ya zargi gwamnatin Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da take haƙƙin ɗan Adam tare da amfani da jami’an tsaro wajen dakile ‘yancin faɗar albarkacin baki.

Lauyan ya ce akwai mutane da dama da aka kama ko aka gurfanar a kotu ba tare da ingantattun hujjoji ba, inda ya yi ikirarin cewa wasu matasa ma an yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru biyar duk da cewa ba a tabbatar da laifinsu ba.

Ya ce daga baya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin, tare da wanke su daga dukkan zarge-zargen.

A cewarsa, mafi yawan waɗanda abin ya shafa matasa ne da ‘ya’yan talakawa waɗanda ba su da ƙarfin ɗaukar lauya domin kare kansu.

Barrista Dantani ya kuma buƙaci Gwamna Zulum da ya sasanta da duk wanda aka tauye masa haƙƙinsa tare da neman afuwa idan har an zalunce shi, yana mai cewa adalci da neman gafara alamun mutunci ne, ba rauni ba.

Ya kammala da cewa: “A ƙarshe, hukuncin Allah shi ne mafi girma, kuma babu wanda zai tsere masa.

“Wakiliya ta lura cewa waɗannan zarge-zarge ra’ayi ne da ikirarin Barrista Hamza Nuhu Dantani. Gwamna Babagana Umara Zulum ko gwamnatin Jihar Borno ba su mayar da martani kan waɗannan zarge-zarge a cikin bayanin da aka wallafa ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img