Tinubu Ya Amince da Ƙara Rundunonin Sojojin Najeriya Zuwa 12, Za a Dauki Sabbin Sojoji 28,000
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da faɗaɗa tsarin rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya daga rundunoni (Divisions) takwas zuwa 12, a wani mataki da gwamnatin tarayya ta ce zai ƙara ƙarfafa tsaro da inganta yadda sojoji ke gudanar da ayyukansu a faɗin ƙasar.
A cikin sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Alhamis, gwamnatin ta kuma bayyana cewa Tinubu ya amince da ɗaukar ƙarin sabbin sojoji 28,000, tare da ci gaba da samar da sabbin makamai, kayan aiki da inganta walwalar jami’an soji.
Sabon tsarin zai ƙunshi rundunoni 12 da za su kasance a Kaduna, Ibadan, Jos, Makurdi, Port Harcourt, Maiduguri, Sokoto, Ilorin, Jalingo, Legas, Enugu da Benin City, inda sabbin rundunonin da za a kafa a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin City ake sa ran za su taimaka wajen inganta jagoranci, saurin kai ɗauki, kare iyakoki, da kuma ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.
Sanarwar ta ce za a aiwatar da wannan shiri ne a matakai biyu. Mataki na farko, wanda ya haɗa da kafa rundunonin 5, 9 da 10, zai kammala kafin watan Satumban 2026, yayin da mataki na biyu da ya haɗa da kafa Runduna ta 83 zai kammala kafin ƙarshen Disamban 2026.
Shugaba Tinubu ya yabawa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Ibrahim Shuaibu, da dakarun sojin Najeriya bisa jajircewarsu wajen kare haɗin kan ƙasa, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari domin tabbatar da sojojin Najeriya suna da kayan aiki, ƙwarin gwiwa da ƙarfin da ake buƙata wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.





