FCCPC Za Ta Binciki Meta, Google, X da Kamfanonin AI Kan Zargin Take Hakkin Kafafen Yaɗa Labarai

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Kare Gasar Kasuwanci da Kare Haƙƙin Masu Amfani ta Tarayya (FCCPC) da ta fara bincike kan manyan kamfanonin fasaha da kuma dandalan Basirar Wucin Gadi (AI) da ke aiki a Najeriya.

Matakin ya biyo bayan ƙorafin da Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai ta Najeriya (NPO), wacce ta haɗa da NPAN, NUJ, BON da GOCOP, ta kai wa Fadar Shugaban Ƙasa. Ƙungiyar ta zargi kamfanoni irin su Meta, Alphabet Inc. da X da yin wasu ayyuka da ka iya tauye gasa tare da amfani da labaran kafafen yaɗa labarai ba tare da adalci ba.

Shugaban FCCPC, Tunji Bello, ya ce binciken zai kasance mai zaman kansa, adalci da kuma dogaro da hujjoji, inda za a bai wa dukkan ɓangarorin damar kare kansu kafin a cimma matsaya.

Hukumar za ta binciki ko akwai karya Dokar FCCPA ta 2018, ciki har da zargin amfani da labarai da sauran abubuwan da ‘yan jarida suka samar wajen horas da tsarin AI ba tare da izini ba, da kuma ko kamfanonin fasaha sun hana kafafen yaɗa labarai damar samun diyya ko yarjejeniyar kasuwanci mai adalci kan amfani da bayanansu.

FCCPC ta tuna cewa a baya ta ci shari’a kan Meta kan wasu laifuffuka da suka shafi dokar kare masu amfani, inda aka ci tarar kamfanin dala miliyan 220, duk da cewa har yanzu kamfanin ya ɗaukaka ƙara.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img