EFCC ta kama shugabar mata ta City Boy Movement
Daga Wakiliya
Hukumar EFCC ta kama Halimat Adenike Tejuosho, tsohuwar mai kula da sashen mata na City Boy Movement a Kudu maso Yammacin Najeriya, kan zargin zambar kudi,
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce an kama Tejuosho tun ranar 8 ga Satumba, kuma har yanzu tana hannun hukumar.
A watan Afrilu ne EFCC ta bayyana Tejuosho a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo, bisa zargin cewa ta karɓi kuɗi daga wasu mutane bayan ta yi musu alkawarin samo musu mukaman gwamnati da kwangiloli.
Hukumar ta ce ta taɓa bincikar ta a watan Yunin 2025 kan zargin amfani da takardun bogi da wasiƙun naɗi na ƙarya wajen yaudarar waɗanda ake zargin ta karɓi kuɗinsu.
Bayan bayyana sunanta a cikin waɗanda ake nema, City Boy Movement ta dakatar da ita daga muƙaminta domin bai wa binciken damar gudana ba tare da katsalandan ba.




