UNGA: “Kun iya magana kan Falasɗinawa, Amma kun yi Shiru Kan Kisan Kiristoci” – Dachomo ya caccaki Gwamnatin Najeriya
Daga Wakiliya
Fasto Ezekiel Dachomo ya soki gwamnatin Najeriya kan abin da ya ce rashin magana kan kisan Kiristoci a Najeriya a yayin jawabin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Faston ya yi wannan magana ne yayin jana’izar wasu mutane uku da aka kashe a wani hari kusa da Jos, inda ya ce gwamnatin Najeriya ta yi magana kan batun Falasɗinawa, amma ta yi shiru kan abin da ya kira tsananta wa Kiristoci a Najeriya.
Dachomo ya kuma gode wa Shugaban Amurka Donald Trump kan yadda ya ce ya tabo batun halin da Kiristoci ke ciki a Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.




