Gwamnatin Kano ta dakatar da hawan dawakai da duk wata Durbar
Daga Wakiliya
Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da dukkan jerin gwanon Durbar da kuma hawan dawakai a cikin birnin Kano har sai baba-ta-gani.
Gwamnatin ta ce an dauki matakin ne bayan wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na jihar, inda aka duba halin tsaro da ya dabaibaye shirye-shiryen gudanar da ayyukan.
A cewar gwamnatin, akwai dimbin magoya baya da aka tattara domin ayyukan, lamarin da ya haifar da fargabar yiwuwar rikici da kuma barazana ga rayuka da dukiyoyi.
Ta umarci jami’an tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar, tare da yin kira ga al’ummar Kano da shugabannin gargajiya da ’yan siyasa da magoya bayansu su zauna lafiya tare da bin umarnin gwamnati.




