Dan wasan Najeriya Nwabali na dab da komawa buga wasa a Saudiyya

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Mai tsaron ragar Super Eagles, Stanley Nwabali, na dab da kulla yarjejeniya da wata ƙungiya a ƙasar Saudiyya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Soccer Laduma ta Afirka ta Kudu ta ruwaito cewa wata ƙungiya daga Saudiyya ta nuna ƙwarin gwiwar ɗaukar Nwabali, duk da cewa wasu ƙungiyoyi daga Isra’ila sun taɓa nuna sha’awar sayensa.

Ana sa ran za a kammala cinikin kafin fara sabon kakar wasa.

Nwabali, mai shekara 30, bai da ƙungiya tun bayan rabuwarsa da Chippa United ta Afirka ta Kudu a watan Fabrairu.

Idan cinikin ya tabbata, hakan zai ba shi damar komawa taka leda bayan watanni yana zaman jiran sabuwar ƙungiya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img