Daga Wakiliya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karɓi kaso na farko na bashin dala biliyan 1.5 daga cikin bashin dala biliyan 5 da ta amince da shi tare da babban bankin First Abu Dhabi Bank na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Rahotanni sun ce za a yi amfani da kuɗin wajen aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2026, gina manyan ayyukan more rayuwa da kuma biyan wasu basussukan da ake bi.
Sai dai, Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da kamfanin tantance ƙimar bashi na Fitch Ratings sun nuna damuwa kan irin wannan tsarin lamuni, suna gargadin cewa yana da wahalar sa ido a kansa kuma zai iya ɓoye ainihin yawan bashin da ƙasa ke bin bashi.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, Najeriya za ta jinginar da takardun bashin gwamnati da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 6.65, domin samun cikakken bashin dala biliyan 5.
Masana sun yi gargadin cewa idan darajar waɗannan kadarori ta ragu, Najeriya na iya fuskantar ƙarin matsin lamba wajen samar da wasu kadarori a matsayin jingina.
A cewar gwamnati, wannan tsari zai taimaka wajen samar da dalar Amurka cikin gaggawa ba tare da sake fitar da sabbin takardun bashi na ƙasashen waje ba.
Ya zuwa ƙarshen shekarar 2025, bashin gwamnatin Najeriya ya kai dala biliyan 110.3, kwatankwacin kusan Naira tiriliyan 159.2.





