Bayan Doguwar Soyayya da Ta Ja Hankali: Shahararrun ‘Yan TikTok Jarvis da Peller Za Su Yi Aure Ranar 1 ga Agusta, 2026

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Fitattun masu ƙirƙirar abubuwan barkwanci a TikTok a Najeriya, Jarvis da Peller, sun sanar da cewa za a ɗaura aurensu a ranar 1 ga Agusta, 2026.

Ma’auratan sun bayyana hakan ne ta hanyar wani gajeren bidiyo mai kayatarwa da suka wallafa a shafukansu na sada zumunta, inda aka rubuta a ƙarshensa: “Jarvis & Peller 01-08-2026.”

Sanarwar ta jawo ce-ce-ku-ce da taya murna daga masoyansu, yayin da bidiyon ya bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta.

Jarvis da Peller na daga cikin fitattun masu ƙirƙira a Najeriya, inda suka shahara da bidiyoyin barkwanci, shirye-shiryen kai tsaye (livestream) da kuma abubuwan da suka shafi soyayya, lamarin da ya ba su miliyoyin mabiya.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ma’auratan ba su bayyana ƙarin bayanai game da bikin auren ba, illa ranar 1 ga Agusta, 2026 da suka sanar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img